ina so a yi wasan dambe,amma banda cuta, kowa ya yi da wanda yake bi,misali, kai...(ya kira wani matashi da ba zai wuce ashirin da biyar ba, sannan ya kira wani da yake sa'an shi) kai ma zo nan, kunga shekarun ku kusan daya ne, kuma muqamin ku ma  anan wajen, kusan d'aya ne, to ina so a yi dambe, sai d'aya ya gaji ya ce ya isa haka, amma in ku na ganin ku ragwaye ne, duk zan halbe ku na sake sabon zubi"

Kafin Lawwali ya gama rufe baki har sun fara kasa kan su, kowa da wanda zai kara da shi.

"Habaa ba kowa ne zai yi ba, in an ka ce kowa ne zai yi tau su waye 'yan kallo?"

Mutum hudu kawai ya zaba, wato No 2 da No 3,sai No 4 da No 5.

"Wadanga, su ne manya wajen ga ko?"

Cikin d'aga murya da ihu suka amsa, da

"Ehhhh su na Oga"

"Tauuu su na zasu nishadantar da mu yau,...kaii Yakubu, taho kai na alqalin wasa, kai zaka bada damar farawa, sharadi daya ne, banda halbi, amma komi ana iyawa, a yi dambe har sai d'aya ya buga qasa so uku, sannan za a qare"

Habaa mana waje fa ya dau harami, sai ihu da murna ake, su kan su wanda za su yi damben ba alamar bacin rai a tattare da su, nan da nan kuwa suka shirya, No 2 da No 3 suka shiga tsakiyar fili, Lawwali na zaune ya na taune cikin bakin shi, idan plan din shi ya tafi daidai, daga yau No 1 ze fara cin qaniyar shi a hannun shi.

Mai kula da wasa tini ya harba bindiga bayan ya sanar da wasan ba wani doka, ana iya amfani da komai dan kare kai, amma banda bindiga.

Kokawa kuwa da naushi, tare da harbi da qafa kamar 'ya'yan jakkai tuni ya kaure a tsakanin su,sun jima suna fafatawa kafin No 3 ya buga qasa ya na haki da fidda numfashi da kyau,

Ihu da murna tare da tafi ne ya kaure a wajen, No 2 ne ya je gaban Lawwali ya duqa ,shi kuma ya daki kafadar shi cikin jinjina, da karrama wa, ihu wajen ya sake dauka, a fuskar No 3 babu alamar jin haushi ko hassada dan an samu nasara akan shi, tabbas har cikin ran su wasa suka dauki abun.

No 4 da No 5 ne suka shiga fili, aka fad'a masu sharadin wasa, tare da harba bindiga, nan da nan suma suka kaure, ana yin nasu ne, wani  matashin da Lawwali ya radawa abinda yake so ya yi, ya fara bi d'aya bayan d'aya ya na fada wa mutane magana a kunnuwan su.

Cikin rabin awa No 4 da No 5 sun jigata, ba wanda ya samu nasara akan dan uwan shi,amma fa kowanne a cikin su ya daku, banda jini ba abinda ke fita a jikin su su dikan.

Cikin hargowa wajen ya dauki sunan, Oga da No 1, cike da mummunan tashin hankali No 1 ya fara kada kai, ya na ja da baya, kamar wani tsumma haka wani gabjeje a wajen ya wurga shi tsakiyar fili, No 1 ji ya yi kamar zai fitsari a wando tsabar tsoro, kowa ya san Lawwali a wajen, ba shi da na biyu a qarfi, ba shi da Mahadi a qarfi a wajen, to akan me za su hada su? Indai ba so suke a kashe shi ba.

Wani irin fushi ne ya bayyana a saman fuskar Lawwali na irin quncin da ke cikin ran shi, cikin qanqanin lokaci ya kawar da fushin ya fara nuna kawai a bar wasan, kar ya cutar da No 1, dariyar yaqe No 1 ya fara, tare da fadin,

"Oga ya ce a bar wasa haka nan, sai wani lokaci"

A gaggauce Lawwali ya kalli matashin da ya yi wa rad'a, ai kuwa matashin ya yi tsagal ya ce,

"Bamu jiya ba mu dai, mu na so mu ga hwadan manya, zai fi dadin kallo,"

"Muna so, mu ma mu na so, mu na son ganin fadan manya!!!!"

Shi ne abinda mutanen wajen ke ta ihu su na maimaita wa, har suka jawo hankalin mutanen da ke rufe a wajen, ta window da duk wata kafa da za su samu damar kallon me ke faruwa suke leqe, ai kuwa cikin daga hannu d'aya wajen ya yi tsit.

Lawwali ne ya isa gaban No 1 ya ce,

"Kar ka damu aboki na, kawai ka dage, wataqila ka samu nasara akai na, ka ga ba ni da wani qarhi Mubaraka ita ta qarhi na ka sani, gashi ban gane ta ba, za ka iya nasara akai na cikin sauqi"

Wata iriyar zufar saman hanci da saman lebe No 1 ke yi, gashi ya na jin wani ruwa na gangarar masa ta qafafun shi, be gama tantance shin fitsari yake a tsaye ba ko kuma zufa ce, ya ji ana karanta sharadin damben,kafin ya ja baya an harba bindiga, zare ido ya yi, ya na kallon Lawwali, wanda fuskar shi ta sauya, daga fara'a zuwa tsantsar bacin rai, hankalin shi ne ya sake tashi.

Kwasa ya yi a guje zai gudu, Lawwali ya cafke shi, wani irin naushi ya kai ma No 1 sai da ya juya, tare da kifewa a qasa, qoqarin buga hannun shi yake a tashi wasan dan ya san ba zai debi komai a jikin Lawwali ba, Lawwali ya bi hannayen ya taushe, ya hana shi buga su.

Dambe ya yi dambe, No 1 ya daku iya duka, duk wani haushin shi da Lawwali ke ji, sai da kaso mai tsoka ya ragu, sai da ya zamana hatta da tsayuwa No 1 ya kasa, baya iya d'aga yatsan shi ko d'aya, ballantana ya buga qasa, idanun shi sun kada sun yi jawur kamar ya yi taruwar jini a cikin su.

Lawwali da kan shi ya d'aga hannayen shi biyu, ya miqe daga saman No 1, ya tabbata dukan da ya masa sai ya sanya shi jinya ta aqalla sati daya,ya ga ta fita yawon cin amana.

Umarni ya bawa No 4 da ya yi jinyar No 1, cikin azama, No 4 da shi ma yake a jikkace, ya fara qoqarin daga No 1, wata qara ya saki mai qarfin gaske, da sauri no 4 ya sake shi, ko da ya duba sai ya ga ashe No 1 ya samu karaya ne, har hannun ya kumbure, da damar matasan wajen sun ji dad'in dukan da aka yi wa No 1 dama ya addabe su, ya ishe su, tunda Lawwali ya koma kwana da zama a cikin gari No 1 ke musu mulkin kama karya, yanzu gashi an yi musu maganin shi.

Lawwali bai kwana a wajen ba, gida ya tafi, ko da ya isa wanka ya fara yi, sannan ya ci abinci ya zauna a kujera, ya na kallon hotunan Mubaraka, da video da ya dauke ta.

Ya na kalla ya na murmushi, tare da jin dad'in sanin inda take, da kuma halin da take ciki,kulawa ta musamman No 4 yake basu,da taimakon Lawwalin.

Duba time ya yi, ya ga sha d'aya saura, bai wani dogon tunani ba kawai ya danna number'n ta, ta yi ringing sau biyu kamar jira take ya kira, ta dauka,

"Hello"

"Assalamualaikum"

Maida ido sama ya yi, kafin ya amsa sallamar da,

"Wa'alaikumussalam, ran ki shi dade baki kwana ba?"

"Ban yi kwana ba, kai mi ka kai da ba ka yi kwana ba har yanzu? Gobe akwai aiki fa, in muka tashi har wata unguwa za mu tai, last 3days an shiga an yi musu barna, ba kadan ba, mutan garin har wasun su sun yi hijira, qalilan ne ke zaune a garin, saboda basu da wajen zuwa"

Sarai ya san ko ina ne, duk da ba su suka yi aikin ba, amma dai abokan aiki, ai ba sa buya.

"Allah shi kai mu,"

"Ameen, me ya sa ka kire ni yanzu? Akwai wani abu ne?"

Shiru ya ɗan yi na wasu seconds kafin ya ce,

"Babu komi, kawai dai na yi kewar ki ne"

Kwanciyar ta ta gyara, tare da sake manna wayar a kunnen ta, ta na jin yanda Muryar shi ta cikakkun mazaje ke dukan dodon kunnen ta,

"Mun fa hadu d'azu"

"Ehh sanin haka ne ma ya sa na ji duk na yi kewar murmushin ki mai tsadar nan, yau baki yi min shi ba sai sau biyu kacal, gaskiya ban qoshi ba, a qara min,"

Wata iriyar siririyar dariya ta dinga yi, har zuciyar shi bai jin komai game da dariyar ta a yau d'in ,soyayyar da ya fara mata kafin ya san me mahaifin ta ya masa, yanzu ta fara sauya salo, ta koma soyayyar daukan fansa.

"Kaiiii ran ki shi dad'e gaskiya sai da sahe, wagga dariya zata hana min kwana"

"Me ya sa za ta hana ma kwana?"

"Saboda in na kwanta zan dinga tunanin ta, kuma zan ji ina son saurarar wata makamanciyar ta daga gare ki, gashi na sani har abada ba aure a tsakanin mu"

Da sauri ta gimtse fuska, tare da mamakin dalilin da zai sa ya ce ba aure a tsakanin su

"Mi ka ka nuhi? An haramta aure a tsakani na da kai ne ko mi?"

"Ba a haramta ba a musulunci, amma iyayen ki sun haramta shi, sanin kan ki na ba mai barin ki auren driver ko? Ban taba baqin cikin rashin ilimin boko ba da na arabiyya sai yanzu, da ina da ilimi da iyayen ki sun bani ke,......ina son ki sultana"

Tsigar jikin ta ce ta tsaya ta mimmiqe, ji ta yi bugun zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri.

"Da gaske ka na so na?"

"Kwarai da gaske, ina son ki Sultana"

Rintse idon ta tayi, tare da cizon leben ta na qasa,cikin lallausan murmushi ta ce,

"Dan Allah maimaita in ji"

"Inda son ki sultana"

"Ka same ni kuwa, ba abinda zai hana ka aure na,"

"Akwai shi,"

"Me ne ne shi?"

"Iyayen ki, iyayen ki musamman Hajiya bata bari ki auri jahili, kuma driver,"

"Auwal ka dena kiran kan ka da wannan mummunan suna, in baka fad'a cewar baka je makaranta ba, babu wanda zai ce baka je ba, and na ji labarin har saukar qur'ani  ka yi, kuma ka fara Makarantar boko itama, to ka ga kenan kai ba jahili bane,"

"Hummm ba zaki gane ba, bari na bar ki ki yi kwana, amma fa ki sani iyayen ki ba za su bar ki aure na ba, ni dai abu guda nis-sani, ke kadai ni ke so, ke kadai nit-taba burin mallaka a matsayin matar da zan aura, bayan ke ban taba son kowa ba, .....Ina son ki Sultana"

Idanun ta a rufe hawaye na kwaranya a idon ta, ya gama zuba kalaman shi masu zafi da kuma dad'i a gare ta, ya kashe wayar shi  ya barta cikin yanayin da ta kasa fassarawa.

Shin da gaske yake iyayen ta ba za su bari ya aure ta ba? Me ye dalili? A duniya mutum na iya auren duk wanda yake so, se wanda musulunci ya hana, misali mace ta auri mace, ko namiji ya auri namiji, ko mutum ya auri wata dabba ko wata halitta, ko musulmi ya auri kafuri,ko muharramai su auri junan su, amma Indai akwai so da qauna kowanne namiji zai iya auren macen da yake so, haka ma mace za ta iya auren namijin da take so, to me ya sa ita zata zama daban a cikin mutane? Saboda kawai shi din driver ne?

Da wannan tunanin bacci mai cike da rudanin tunani ya dauke ta.

*************************

Duk abinda aka sanyawa rana, wannan ranar zata zagayo, ko ayi abun, ko kuma a fasa shi .

Yau ce ranar zabe, gwamna da iyalin shi tun asuba suka shirya suka je wajen yin zaɓe, sun dangwala nasu sun koma government house, yau har da sultana aka tafi, ta na can ne kawai, amma hankalin ta baya tare da ita, rashin ganin Auwal na damun ta, tun randa suka yi waya, yau kwana hudu, ta ji shi shiru, shin ko dai ya rabu da ita ne saboda tunanin Hajiya ba zata yarda ba, daddy ma ba zai amince ba? Amma ai bai ce zai rabu da ita ba.

Wannan tunanin sun ma ƙwaƙwalwar ta yawa, har ya fara sanya ta zance a fili, cikin rashin fahimtar me ta fada Sultan ya ce,

"Mi kin ka ce? Wa ye zai bar ki?"

Da sauri ta hau yaqe ta na barin wajen, tare da sanar da shi ,

"Ba kowa, ba komai, kar ka damu, ina zuwa"

Tafiya kawai take a tankamemen gidan da ya cika da mutane kala kala, duk ta gama ratsa su ta wuce wani building, ba abinda ke tashi a hanyar wajen se karar takalmin ta, wayar ta ta tsaya cak ta na latsawa, sama sama ta ke jin muryoyin su,

"......ka tabbata dai ka saka a kawo takardun zaben da aka dangwala ko? Na hwadi maka in banda aikin da Sultana ka yi a gari, sai d'an wanda munka hwara shekarar ga, walle ba mai zabar mu,"

"Ki kwantar da hankalin ki Hajiya, na gama komai, akwai taqadarin yaro na da ka yi min aiki ko wanne iri na, shi da yara nai, ke ko batar da mutum nicce ayi, ba shi koma second d'aya raye indai yaron nan na saka, ke duk wasu abubuwa da ki kaga ina yi da shi ni ka taqama, dan haka zabe kamar na ci na gama ne,"

Wata iriyar dariya suka sanya a tare, suka ci gaba da hira, Gwamna na bawa Hajiya Ikee labarin Lawwali, ba tare da ya sanar da ita sunan shi ba, sai jin dad'i take ta na addu'a Allah ya sa su zarce.

Qoqarin komawa cikin mutane suke, cikin sauri Sultana da ta daskare a wajen ta cire takalmin ta a hannu, ta fad'a wata qofa da ta gani a dan bude ta b'uya, Hajiya Ikee ce da Gwamna Halliru suka fito, cikin farin ciki, sun sha ado na alfarma, sai walqiya suke, da qamshi.

Su na wuce wa sultana ta sanya wani irin kuka mai ban tausayi, mahaifan ta ashe basu da imani? Kuma a haka suke neman su ci gaba da jagorantar al'umma?...........

*Ni Ko nace iya abinda ki ka sani ma kenan 'yannan, ba ki san kalar tsafin da gyatumi ke yi ba*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH

PAGE 33:



Lokuta da dama idan farin ciki, ko baqin ciki ya dami mutum, akwai mutum na farko dake zuwa zuciyar wannan mutumin, walau wanda ya yarda da shi ko da ba 'yan uwantaka ta jini a tsakanin su,ko kuma wanda ke da alhaki akan halin da mutum ya shiga, masoyi shine mutum na farko da ke fara zuwar wa mutum a rai, mace ko namiji, qawa ko saurayi, miji ko mata, ko kuma iyaye.

A baya Sultana ba ta da wanda ya wuce Sultan a wajen ta, saboda shaquwa irin ta yaya da qanwa da ke a tsakanin su, komai nata shi take sanarwa, to amma tunda shi Allah bai sa har yanzu ya gano asalin mummunanan dabi'un mahaifan nasu ba, ba ta so ya sani, kamar yanda suka so ya yi rayuwa haka yake yi, ba ya saba umarnin su, ya kai a ce ya ajiye iyali, amma rayuwar shi abar juyawa ce a hannayen su, gwanda ita sun bata 'yanci, wanda a wajen ta ba 'yanci bane, sun yi amfani da abinda suke kira 'yancin su na biyan buqatar su ta son zuciya da shi.

Lawwali ne babban wanda za ta iya wannan maganar sirrin da shi, (to wai ma makaranta mu dan tattauna wani abu mana, shin daidai ne kawai daga yin saurayi, dan ki na jin kin yarda dashi, dari bisa dari, sai ki ta fada masa sirrin ki? Musamman wannan babban sirrin? 'yan mata da dama su na shirme, da yarinta, kawai yanda ke ki ke jin ki na son namiji, To haka ki ke dauka shima haka yake son ki, kuma yanda kk yarda da shi shima haka ya yarda da ke, wallahi ba haka bane, maza kala kala ne,kashi kashi ne,akwai wanda zai so ki kamar ran shi, amma ba sirri, nashi sirrin ma be riqe ba balle na wani, kuma zai iya rufe ido ya manta da son da yake maki, ya kafta maki uba uban rashin mutunci, daga baya in kun shirya ya baki hakuri, ke kuma ya wuce, anjima ma in wani abu ya taso se kin fada masa. Akwai namijin da zai so ki, kuma zai saurare ki, zai taya ki warware matsalar ki da damuwar ki,zai shiga lamarin ki kamar nashi, kuma ze riqe miki sirrin ki,amma ki sani 'yar uwa irin su basu da yawa a wannan zamanin, wani ma Allah Allah yake yaji maganar ki ya fadawa yan uwan shi da abokan shi, ki na nan tanyare bude a faranti kowa ya san sirrin ki da na 'yan gidan ku, a kiyaye, a dena makahon so)

Wayar shi take ta nema, ana fada mata busy, cikin bacin rai, da sharar hawaye ta bar taron, iyayen nata basu son video ko camera su hau kan ta, ganin yanayin da take ciki, dan haka suka basar sukai ta harkokin su, direct motar ta ta nufa,ta na qoqarin shiga, wani murdadden namiji da baqaqen kaya, da baqin gilashi ya tsaya a gefen ta ya ce,

"Ran ki shi dade, Excellency ya ce kar a bar ki ki hita yanzu,sai an fadi sakamakon zabe gari ya lafa,sannan za ku fita,yanzu ki tai zuwa sashen ku,"

"Saqo ka ke bani ko umarni?"

"Ran ki shi dade, ba umarni bane, dan Allah ki taimake mu ki koma, abincin mu na nan, ke mai tausayi ce, kar ki fita ya zama sanadin barin mu aiki"

Kallon shi tayi, ta gan shi rusheshe, ko a ka aka ce ya maida ta sashen, cikin qiftawar ido ya na iyawa, amma ya gwammaci ya yi amfani da kalamai masu taushi a gare ta, cike da baqin cikin ci gaba da zama a gidan Gwamnatin ta shiga gaba, ya na take mata baya, har bangaren su, ta na shiga ta rufe da qarfi ta saki wani irin kuka, mai matuqar kuna.

"Anya su Daddy za su hadu da rahamar Allah kuwa? Ashe duk abinda Daddy ke aikatawa, Hajiya ta yi kamar bata sani ba ita ka zuga shi aikata wasu munanan aikin? Anya iyayen ga namu su na da imani kuwa? Sun san Allah kuwa?"

Kuka take ta na surutai ita kadai,ga wayar Lawwali
Showing 63001 words to 66000 words out of 150481 words