kai waje, cikin fada ya juya ya ce,

"Ke dayalla can ki koma gida ki zauna gani nan zuwa yanzun ga"

Wayar shi ya kalla dan yin magana ya ga an kashe kiran, bin kiran Lawwali ya dinga yi amma ba a dauka ba, tashin hankalin da ya shiga ba abun kwatanta wa bane, balle misali, da kyar ya ke ganin inda yake sanya qafar shi, kiran waya ya dinga yi, ya na dakatar da neman Mubaraka ta kowanne bangare.
Video'n yanda Lawwali ke ganawa wanda suka kama azaba ne ke gilmawa a idon gwamna, Muryar Sultan da Sultana sun cika masa kunne ,hango su yake a yanayi na azabtuwa da uqubar Lawwali.

Kafin ya kai jikin motar shi,jiri ya kwashe shi, ya fadi a qasa,drivern shi da securities ne suka daga shi aka sanya shi a mota, asibiti aka nufa da shi direct dan kuwa ba ya motsi.

Hajiya Ikee kuwa kuka take ta na qarawa, tare da tsinewa Lawwali albarka.

*********

A can daji kuwa Lawwali da Sultana sun bawa Sultan labarin duk abinda yake a boye a gare shi, na shekara da shekaru, har da wanda basu sani ba ma, sai da Lawwali ya basu.

Duk dauriya da qarfin zuciya irin na Sultan sai da ya yi kuka, da wahala ya yi kuka akan abu, sai dai a ga jijiyoyin kan shi na tashi, a ga idanun shi sun yi ja jawur, amma banda kuka.

Zuciyar shi ta gama karyewa, yanzu ace duk mahaifin shi ke aikata wadannan mugayen laifukan saboda son duniya da abinda ke cikin ta? Saboda siyasa da son mulki? To me ya tanadar wa kan shi a lahira? Me ya ke aikatawa na gari wanda Allah zai yafe masa wadannan mugayen laifukan? Shin mahaifin su musulmi ne kuwa? Ya na tantamar imanin shi da Allah, wanda ya ce Allah shi ne Ubangijin shi, Annabi Muhammad shi ne annabin shi, qur'ani da Hadith ne littafan da ya yadda su zama madubin shi, ba zai aikata shirka ga Allah ba, ba zai aikata abubuwan da gwamna Halliru Murtala Gusau ya aikata ba.

Miqewa ya yi ya fice daga wajen, bai san ina yake tafiya ba, kawai sai ganin shi ya yi, a wajen mutanen da aka kamo,a cikin hasken solar da aka sa a wajen yake hango wasu har da jariran yara a hannun su, wasu da ciki, wasu kuma gasu nan a wahale saboda hana shan kwaya da giya da Lawwali ya yi.

Hawaye ne kawai ke zuba a idanun Sultan da sultana dake take masa baya, Lawwali kuwa na tsaye ya na hango su, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, to meye amfanin wannan rayuwar mara mamora?

Shi nashi iyayen su na can hankalin su kwance, basu damu da shi ba, basu damu da halin da yake ciki ba shi da qanwar shi, anya kuwa da ake cewa ba wanda zai haifi d'a a cikin shi ya qi shi gaskiya ne? Domin shi gashi ya gani da idanun shi, shi shaida ne,iyayen su basu damu da su ba, jiya ya amsa kiran 'Dan Talo ya na washe baki, wai gwamna ya ce ya bada hoton mubaraka sati Uku da suka gabata, wai gwamna ya mata miji, kuma sun ji shiru, ko zai bincika a ji me ke faruwa, a qarshe ya fara masa qorafin basu da abinci su da bisashen shi (awakin shi) gashi su Lamishi sun dena zuwa aiki,tunda yanzu su gwamna surukan su ne, be kamata su na zuwa aiki gidan ba.

Sai da Lawwali ya gama jin surutan Dan Talo ya fada masa jimla daya wato "Ku saida bisashen ku ci abinci" sannan ya  kashe wayar shi.

Jikin wani kututturen itace Sultana da Sultan suka zauna, hannun su na cikin na junan su, sultana ce ta kwantar da kan ta a kafadar Sultan, ta share hawayen ta da ke zuba, ta ce,

"Yah Sultan ka ga rayuwar da iyayen mu suke aikatawa, a tunanin su dan jin dad'in mu suke yi, su na quntata rayuwar wasu bayin Allahn, su na haskaka ta mu,"

Sultan ya kasa magana har a wannan lokacin, wani abu yake ji ya tokare masa maqoshi ya qi wucewa.

Hannu ta sanya ta na ta shafa bayan shi, a hankali ya ke sauke ajiyar zuciya, cikin wata iriyar Murya mai rauni ya ce,

"Iyayen mu sun halaka, sun biye wa son zuciya, da son duniya sun halaka, ya Allah mai shiryar wa ka shiryar da su, ka yahe musu zunuban su,...sultana yanzu ina Daddy zai kai haqqin rayukan da ya salwantar?"

Wani irin kuka ne mai maqaqi da zafi a wuya ya turniqe Sultan, tausayin shi ya gama kashe zuciyar Sultana, wannan halin da zai shiga take tsoro tun farko, saboda ta san he is very sensitive kamar ta, har ma ya fi ta.

Su na nan zaune, Lawwali ya je wajen nasu cikin murna, ya sanar da Sultana mahaifin su ya janye neman Mubaraka da ake yi, amma fa ya na kwance a asibiti ba lafiya.

Hankulan su ya tashi, da jin mahaifin su ba lafiya, shi kuwa ya na sanar da su, ya tafi ya na neman layin No 4, yanayin network din wajen akwai matsala, dan haka da kyar ya same shi, ya na dauka ya ce,

"Gobe da subahi ku taho, hanya lahiya lau ne yanzu"

"To Oga Allah shi kai mu"

"Ameen, lahiya kuwa Taheer? Akwai damuwa ne?"

Da sauri No 4 ya daidaita Muryar shi ya ce,

"Lahiya qalou Oga, kwana na hwara shi ya sa ka ji murya ta haka nan"

"Tau yayi, ka sanar da Barakana gobe mu na tare, ba na so na kira ta yanzu na san ta yi kwana"

"To Oga zan isar da saqon ka, kahin mu taso ma ai na san za ka kire ta ko?"

"Kwarrai da gaske, sai goben"

"Tauu Allah shi kai mu"

"Ameen"

Cikin murna ya fada dakin nasu,  Sultana da Sultan ya gani har sun riga shi isa dakin, su na jayayya akan zuwa ganin mahaifin su, Sultana na bawa Sultan hakuri, akan ya bari ba yanzu ba, shi kuwa ya dage sai ya tafi.

Lawwali ne cikin nuna halin ko in kula, dan ba wai ya ji wani abu bane dan gwamnan na asibiti, budar bakin shi ya ce da Sultan

"Ka ga Suruki na Sultan, na san kai mai addu'a ne da ibada, amma wagga qaddara kai ma ta kamma, ba ka tahiya ko ina, har sai mahaifin ka ya warke ya biya mana bukatun mu, domin ba rayuwar shi ce kad'ai adda mahimmanci ba, mu ma mutane ne"

Lawwali na gama fadin haka ya fita,Sallah ce a zuciyar shi, amma bai san ta yanda zai fara zuwa ya yi alwala ya gabatar da Sallah ba, gani yake kamar in ya yi ba zata karbu ba, kuma ma dai maganar gaskiya, ya na ganin kamar ya manta wasu abubuwan, shekarun da ya dena sallah da yawa, Gashi yanzu Sultan ya zo, ya na neman kawo masa wata maganar komawa gida, ba zai taba barin shi komawa ba, sai ya cika alqawarin dawo da mubaraka wajen shi lafiya.

Dakin marigayi No 5 ya sa aka gyarawa Sultan, ya je ya lallaba shi, akan lallabawar da ya tarar Sultana na masa, ya raka shi har dakin, suka yi sai da safe ya koma nasu dakin.

Alwala ya je ya yi, ya zauna, ya kasa tashi ya tada sallar,Sultana kuwa ta fada duniyar tunanin halin da mahaifin su ke ciki, dan haka bata kula da halin da mijin ta ke ciki ba.

"Uhummm na ce, kin yi sallah ne?"

Da sauri ta zare hannun ta daga tagumin da ta yi,ta kalle shi, dan ta na so ta tabbatar da shin Lawwali ne ya ke tambayar ta tayi sallah ko ah ah, ganin ya kafe ta da ido ya na neman qarin bayani ne ya sa  ta ce,

"Eh na yi magariba kahin Ku zo, amma ban yi Isha'i ba"

"Ok to ki tai ki yi mana, mu kwanta, kwana nika ji"

Tashi ta yi, ta tafi ta yi alwala, duk tunani da damuwa sun addabe ta.

Tada sallah tayi, Lawwali kuwa ya maida hankali ya na kallon me take, da yanda take bin qa'idojin yin Sallah, duk ya na haddace wa a kan shi.

Sai da ta idar ta yi sallama sannan ta kula da kallon da yake mata.

Murmushi ta yi, dan kuwa an ci gaba, in zata shekara Sallah dan ya kalla ma abun ya bashi sha'awa ya yi, ba zai kalla ba, qarshe ma bar mata dakin yake, yau kuwa Gashi sai binta yake da kallo.

"Ka na buqatar wani abu daga waje na ne"

Sunkuyar da kan shi ya yi, cikin jin nauyin ta, ya ce,

"Ki koyar da ni yanda  aka yin sallah"

Gyara zaman ta tayi sannan ta ce,

"Ba a jin kunyar tambaya a addini, duk girman mutum duk qanqantar shi, duk sanin shi duk rashin sanin shi, a kullum shi mai neman sani ne, dan haka kar ka ji kunya, ni ma har yanzu akwai abubuwan da ban iya ba, ina neman sani akan su"

Nan dai Sultana ta koya masa abubuwan da ya mance.

Ya kuwa yi sallah,ranar Sultana sai da ta yi kukan farin ciki, saboda yanda Lawwali ya jima a sujjada ya na kuka ya na qasqantar da kan shi gaban ubangiji, sai neman gafarar Allah yake ya na kumawa.

Tausayin shi ya gama ratsa duk wata kafa ta jikin ta, ya jima ya na sallar da bai san adadin ta ba, sai da ya ji qafafun shi sun kasa tsayuwa sannan ya sallame, da gudu Sultana ta fada jikin shi, suka rungume juna su na kuka.

Cikin kukan ya ce,

"Ki na ganin Allah zai gafarta min kuwa? Abubuwan da na yi a rayuwa su na da yawa Sultana, rayukan mutane da na dauka da hannun ga nawa su na da yawa, ba zan iya qayyade miki su ba, Sultana wasu lokuta in mun ka kashe gari guda hukuma na qiyasta mutane ne fa kawai su ce an kashe mutum kaza, amma adadin ya hi haka nan, ki na ganin Allah zai yafe wa mai laifi da yawa, kuma manya kama ta?"

Shafa fuskar shi ta yi, ta na share masa hawayen shi, ta kai labban ta da suka bushe saboda kuka, ta manna a nashi, ba tare da ya mayar mata da martani ba, ba tare da Itan ma ta na jiran martanin shi ba, ta daga ta kalle shi tace,

"Allah subhanahu wata'ala ya ce, kar mu yanke tsammani  daga rahamar shi, shi mai rahama ne, Allah subhanahu Wata'ala ya ce, da bawa zai je masa da zunubin da ya kai kumfar teku, ya tuba, tuba mai kyau, to zai gafarta masa dukkan zunubin shi, bawan da Allah baya gafarta wa yake sawa a wuta shi ne, bawa mai shirka, har ya mutu ya na shirka, kuma bai dena ba, to wannan bawan zai dawwama a wutar Allah ne, ba ranar fita, dan haka ina kyautata wa Allah zato, zai karbi tuban ka, da izinin Allah"

Tunda suka zo Hajiya Ikee bata taɓa kiran Lawwali ba sai yau, ringing din wayar ne ya cika dakin, Lawwali ya kalli Sultana, Sultana ta kalle shi.......

*A daga ko kar a dagaaaa????😂*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH



PAGE 52:



Sultana ce ta miqa hannu za ta dauka, Lawwali ya yi saurin janye wa,ya kafe ta da wani mugun kallo, idanun ta ne suka ciko da kwalla, saboda ta na so ta ji a wanne hali mahaifin su yake,ganin idanun ta na qoqarin zubar da ruwa ne ya sanya Lawwali sassauta kallon da yake mata, bin kiran ya yi ba dan ya so ba, sai dan ba ya son duk abinda zai sanya ta zubar hawaye, a handsfree ya sanya wayar, kamar jira Hajiya Ikee take a kira, ta yi sauri ta dauka.

"Hello,...Hello,...Lawwali ka na ji na kuwa? Ka wa Allah, ka wa iyayen ka ka maido min da yaran mu,"

Fashewa ta yi da wani irin kuka, mai ban tausayi,sultana ma kukan take, ba abinda ke tsakanin su da iyayen su illa matsananciyar soyayya da kulawa, duk wani abu da zai sanya su farin ciki su na musu shi, duk wannan halin da suke ciki, dan ganin sun faranta musu ne,sai dai kashhh ba su bi hanya madaidaiciya ba, wannan shi ne babban kuskuren su a rayuwa.

"Ka na ji na kuwa? Don Allah ba dan halin mu ba ka sake mana yaran mu,His Excellency na cikin mawuyacin hali, tunda an ka kawo shi bai san wanda ke kan shi ba, bai san wanda ke gehen shi ba, ko motsi ba shi yi, ka taimaka ka maiso mana da su, ko Allah zai sa shi bude ido"

"Hajiya ki na bata bakin ki,domin ke baki san kala da kalan dokoki da yasa ba,kuma ni ban tab'a tsallake umarnin shi ba, shin su iyayen da munka d'auke Wa yara mun san halin da suke a yanzu? Ko kin san cewa akwai wad'anda sun shekara uku zuwa hudu nan wajen? Akwai wad'anda suke anan wajen tun farkon fara aikin da shi mijin ki yasa mu yi, su to ya iyayen su suke ji? Ke San ciwon ka nemi naka ka rasa? Baka san inda shike ba? Ba za ki sani ba, ni zan baki labari, lokacin da mijin ki yaci amana ta, ya dauken qauna ta, lokacin nan ba irin tashin hankali da u'qubar da ban shiga ba, ashe ta na nan kusa da ni, ban sani ba, ku gode Allah kun san inda suke, kar ki qara kira na,"

Sultana ce ta matsa jikin shi za ta amshi wayar, ya wurga mata wani kallo mai dauke da warning, sannan ya wurga wayar saman gado ita kuma ya dauke ta cak ya dora a saman cinyoyin shi, ya manna bakin shi a nata, ranar Lawwali ya bawa kan shi mamaki, ashe ya iya irin wannan soyayyar bai sani ba.

Sultana kuwa tun ta na kukan hana ta magana da mahaifiyar ta da ya yi, har sai da ta manta kowa da komai, jin ta kawai take a duniyar da Lawwali ya kai ta, mai cike da ni'ima da nishad'i, mai cike da gamsar wa, duk wata nutsuwar da ke tattare da ita ta kwace, ba abinda take gani a idanun ta, sai Auwal din ta, ta na tsaka da amsar saqon salon soyayyar shi mai wuyar fassara ta ji ya na qoqarin cimma burin shi, da sauri ta bude ido, dan kuwa bata gama warkewa ba, kyabe baki ta yi, irin na shagwabar nan, Lawwali ya kalle ta da rinannun idanun shi, da alamar tambaya, sauke idanun ta tayi, ta kalli qasa, ta na wasa da qirjin shi ta ce,

"Da zafi fa, ban warke ba"

Da sauri ya d'aga ta, ya na nuna nadamar abinda yake son aikatawa, ganin hakan da ya yi, sai ya bawa Sultana dariya, hancin shi ta ɗan ja kad'an tare da kai wa lips din shi kiss sau daya ta ce,

"You are so cute,"

Murmushi ya yi sannan ya ce,

"Sannu Sultana, ki yafe min, ban San zaki ji ciwo ba, ko za mu tai gari ki ga likita?"

Kwantar da kan ta tayi a qirjin shi, a ran ta ta na ayyana, da ta san inda aka kwantar da mahaifin ta da sun je asibitin ko daga nesa ne ta hango shi, hawaye ne taji su na zuba a idanun ta, da sauri ta sa hannu za ta goge, lawwali ya riga ta, cikin murya mai sanyi ya ke magana,

"Sultyna ki dena kukan ga, ya na karyar min da zuciya, na ji kamar na faasa abinda na ke da niyya, ke dai san quduri na da yasa na ke abinda nake a yanzu, ki bani goyon baya komi zai wuce,in shaa Allahu"

"Allah ya yarda, ina son ka miji na"

Wani irin dad'i ne ya lullube Lawwali, kalmar da ba wanda ya taba furta masa bayan qanwar shi sai Kuma ita, amma a bakin Mubaraka kad'ai ya fara jin wannan kalma, se ga shi ya samu  matar dake yawan furta masa, yi ya yi kamar bai ji ba ya ɗan had'e gira ya ce,

"Na'am mi ki ka ce??"

Murmushi tayi dan ta gane me yake nufi, so yake ta maimaita masa, tashi tayi ta haye jikin shi, ta kwantar da shi a saman gadon sosai, ta yanda suke fuskantar junan su, sai da ta sumbace shi sosai sannan ta kalli kwayar idon shi ta ce,

"Cewa nayi....ina son hancin ka, da idon ka, da nan wajen..(ta nuna lips din shi) ina son kowacce gaba da ke jikin ka...ina son ka, ko da ace ni makauniya ce, kuma kurma ce, sannan bebiya ce, zan qirqiri kowacce hanya ce dan sanar da kai ni Sultana ina son ka Auwal, ba zan taba dena son ka a raina ba, har sai sanda na dena numfashi a duniya, ina maka son da ban taba yi wa wani ba, kai ne na farko a cikin zuciya ta, kuma kai ne na qarshe"

Wani irin numfashi mai sauti Lawwali ke saukewa ya rasa kalar dad'in da Sultana ke sanya shi ji a wanan lokaci, rungume ta ya yi sosai a jikin shi, har sai da ta saki wata siririyar qara, sannan ya sake ta ya na murmushi.

"Yi hankuri Sultyna, ji nikai kamar na bude fata da tsokar jiki na, na balle qashin da ya yi wa zuciya ta rumfa na ajiye ki a can ciki ki zauna daram, saboda yanda nake jin...."

Shiru ya yi bai furta ba, a hankali ta daga kan ta, cikin wani kallo mai kashe jiki, ta na lasar leben ta na qasa ta ce,

"Me ka ke ji?"

"Ina jin son ki Sultana, ina jin qaunar ki sultana, ba na son rabuwa da ke har bayan mutuwa ta, amma na san zai wahala mu had'u, saboda kowa makomar shi d...."

Ba tare data shirya ba ta ji saukar wasu hawaye Masu zafi, a kuncin ta, dan kuwa ta fuskanci me yake so ya fada,

"Subhanallahi, haba haba Auwal, ka dena kalar wannan tunanin, rahamar Allah mai yalwa ce, Allah ba so ya ke ya sanya bayin shi a wuta ba, Allah so yake bayin shi masu zunubi su tuba domin ya yafe musu, ya lullube su da rahamar shi komai laifin su, wanda ma ya yi shirka ga Allah in ya tuba kan ya mutu Allah na yafe masa ballantana kai, da baka taba duqawa gaban boka ko malam ba, sannan baka sani ba, ni
Showing 111001 words to 114000 words out of 150481 words