ke jiran kiran shi,kallon wayar ta tayi, ta sauke ajiyar zuciya, daga qarshe dai ta tashi ta kai Ahmad dakin su, sannan ta koma ta tashi su Bilkisu.

Rufe ko ina ta yi, ta koma cikin yaran ta ta kwanta, ta yi nisa a bacin ta, ta yi mummunan mafarkin da ya sanya ta tashi a firgice kuma a tsorace............

*Kun dai san mafarkin wasu bayin Allahn na zama gaskiya ko😂🤭🙏🏼*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 54:

Addu'a Hansatu ta yi ta ce,

"A'uzubi kalimatillahi taamat, min galbihi, wa iqabihi, wa sharri ibadihi, wamin hamazatisshayadin,wa'an yahdhurun"

Sai ta juya daga ɓangaren dama da take, ta koma hagu, ta sake cewa,

"A'uzu billahi minas-shaidhanir-rajeem,"

Ta tofa dama da hagu, ta rintse idon ta, bacci fa sam ya gagari idanun Hansatu, dan haka tashi ta yi, ta yi alwala, ta hau yin nafila ba qaqqautawa, ta na neman tsarin Allah akan abinda ta gani cikin mafarkin ta.

Sai da ta ji bacci ya mata yawa a ido, sannan ta yi sallama, ta sanya alarm ta qure volume din wayar, dan kar ta makara sallar asuba.

**************************

Cikin nasara da taimakon Allah, Lawwali ya fara rage mutanen da suka yi garkuwa da su, su na maida su wajen ahalin su, da kudin fansar da suka karba, ba qaramin tanadi Lawwali yayi ba, dan gabatar da hakan.

Mubaraka ta zama mai ban hakuri a duk inda suka je, kusan saboda ita ake kyale su Lawwali, dan kuwa Mubaraka Allah ya hore mata baiwar iya kalamai, masu sanya nutsuwa, Allah ya mata suffar mutanen kirki, ta yanda duk wanda ya kalle ta zai ji ta shiga ran shi, sai dai in mutum ya kai qololuwa a hassada.

A cikin sati biyu, kudi sun fara gazawa, sai da Sultan ya bada gudun mawar shi, Lawwali da ya qi karba, a cewar shi, dole a koma wajen Gwamna Halliru ya biya, ai shi suke bawa kudin ya sammu su.

Sultana kuwa ta ce,

"Daddyn da bai san wa ke kan shi ba, ai ba yanda za ai shi ba da kuddi, a dai yi anhwani da nawa da na Sultan"

Barirah da masu yin girki a wajen, sun kafe su dai za su zauna anan, tunda dama can su an qi sakin su ne saboda ba wanda ya biya kudi a dangin su, ba kuma wanda ya damu da neman su.

Lawwali ya ce sam ba za a yi haka ba, su zauna a daji, a na cikin haka wasu daga cikin matasan wajen maza suka amince za su aure su, Lawwali ya yi farin ciki da hakan sosai.

Dan haka sun yanke shawara za su shiga gari, su nemi wani babban malamin ya daura musu aure.

Sultan kuwa ya musu alqawarin wajen zama a cikin gari.

Ranar an yi wata yar kwarya kwaryan walima a wajen, saboda murnar yanda komai ke tafiya musu cikin sauqi.

Yamma ta yi liss, ana zazzaune a harabar wajen da suka saba zama, Lawwali na tunanin yanda za su yi da makaman nan nasu, shin ma jami'an tsaro za su miqa, wanda tun asali su Gwamna Halliru ke aikowa su kawo musu, ko kuma siyarwa za su yi, ko kuma lahanta su za su yi kar kowa ya amfana da su?

Shawara dai suke ta yi, ba su samu matsaya ba, Mubaraka kuwa tunanin da ke cikin zuciyar ta daban, ta na zauna gefen su, shiruuu ta na tunani, Lawwali ne ya bar cikin yaran nashi ya zauna a gefen ta.

Murmushin yaqe ta masa, shi kuma ya kalle ta da kulawa,

"Barakana me ne ne, ban ganin fara'a ga huskar ki? Ba haka ki ke so ba, na ajiye komai na zama mutunen kirki? Shin ba burin ki ba kenan?"

"Alhamdu lilLAAH, babban buri na ya cika, amma ina da wani burin bayan wanga, kai kuma b'acin rai ne a gare ka, ni kuma ba na so na aikata duk wani abu da zai b'ata ran ka,"

"Barakana me ne ne burin ki? hwada min ko menene, zan cika maki shi, indai bai hi qarhi na ba"

Kauda kan ta tayi, ta share kwallar idon ta, nan da nan kuwa hankalin Lawwali ya tashi.

"Barakana me ne ne, me kike so?"

"Ummana"

Sai ta fashe da kuka, sakin qaramar bindigar da ke hannun shi ya yi a qasa, ya kama ta a gefen hannun shi, ya na lallashin ta, kwata kwata bai da plans din komawa gida wajen lalatatun iyayen su, ya san dama ita kadai zata kawo masa cikas, ta sanya su a rai over,shi kuwa ba sa gaban shi, kamar yanda ya tabbata ba su gaban iyayen nasu.

"Ki dena kuka, zan maishe ki duk inda ki ke so, amma ba yanzu ba"

"Yah Auwal to dan Allah ka kai ni na gan su,tunda na zo na ke tunanin su, yau ji nake kamar ba zan iya ci gaba da numfashi ba in ban gan su ba"

Cikin bacin rai ya kalle ta ya ce,

"Shin ban hana maki maganar mutuwa ba? Mi sunka tsinana maki a rayuwa banda lalacewa da tagayyara? Sun san inda ki ke? Sun damu da ke ne? Ko kuwa ni me ne ne bana maki da ba zaki tattare soyayyar da ki ke musu ki min ita ba?"

Ya na gama fadin haka ya bar wajen rai a bace, mubaraka kuwa kuka ta sanya ta na kiran shi, bai koma ba.

Sultana da Taheer da Sultan ne suka hau rarrashin ta, cikin kuka ta ce,

"Aunty Sultana ki roqar min shi dan Allah,I want to see my parents ,I love them so much, duk da na san ba sa son mu, lokuta da dama ina mamakin me ya sa to suka haife mu in ba sa son mu? Amma ba zan iya dena son su ba, iyaye na ne, komai lalacewar iyaye dole su na da mahimmanci a wajen d'an su, dan Allah ki fahimtar da Yah Auwal, ba wai ba na son shi bane, ina son shi sama da yanda nake son komai da kowa a rayuwa ta, ban da abu mafi mahimmanci sama da shi, amma ina so na ga iyayen mu, na jima kwarai rabo na da su"

Kuka take ta yi, gwanin ban tausayi, su na ta lallashin ta, Lawwali ne ya kutsa tsakiyar su ya rungume ta, ya ce,

"Ni ma ina son ki sama da komai da kowa a rayuwa ta Barakana,ki shirya gobe zan kai ki ki gan su,kalar tarbar da za su miki ita zata sa na barki wajen su, ko na dauke ki gaba d'ai"

Murna ta fara yi sosai, Sultana na taya ta dariya.

Lawwali ne ya kalli Sultana da Sultan ya ce,

"Ku ko jibi in mun dawo, ku na iya zuwa ku ga su Hajiya, amma sai kun min alqawarin ku na dawowa"

Wani tsalle Sultana ta daka ta d'afe su daga shi har mubarakan, sai da suka fad'i cikin yashin wajen,

"Mun maka alqawari mu na dawowa,"

Dariya mutanen wajen sukai ta yi, lokacin sallah ne ya yi, suka tashi dan gabatar da Sallah .

Kowa ka gani fuskar shi dauke da nishadi, banda No 4 dan ya kula da irin kallon da Sultan ke bin Mubaraka da shi,shi kuwa ba ya so.

Bayan sallar Isha'i ne kowa na d'akin shi,  sultana na kwance ta fara bacci a jikin Lawwali, ya kwantar da ita a hankali, ya sauka cikin sand'a ya bude wata locker, laptops guda biyu ya dakko, sai wasu qananan qundin ajiya, da disk din CD guda uku, sai Camera da waya d'aya, sanya su ya yi a gaba, ya na kallo, ya na hawaye.

Sultana da ta farka tun sanda ya sauka, ta Qura masa idanu, cikin ranta ta na ayyana ba zata bari ya aikata abinda yake da niyya ba, ba zata bari ba sam.

Washe gari da safe, Mubaraka tun da ta yi asuba ta kasa komawa bacci, sai murna take, wajen Taheer ta je, ta na ta masa hira, a can ta tarar da Sultan, su na shan dumi, a wutar da suka kunna.

Cikin hasken wutar Sultan ke kallon yanda kwayar idon ta ke fitar da wani irin haske, a zuciyar shi ya ke ayyana dama kar gari ya qarasa waje wa, ya tsaya a haka, dan ya dawwama ya na kallon cikin idon ta.

Taheer na kula da haka kuwa ya hade fuska ya ce ma Mubaraka.

"Ke da kin ka taho nan, ki na surutun banza, da ba zuwa kin kai ki ka shirya kayan ki ba, ki ka sani ko shi bar ki can?"

"Kuma fa haka ne Yah Taheer, ina zuwa"

Miqewa ta yi cikin azama, da murna kamar qaramar yarinya, Taheer kuwa da sauri ya ce,

"Ki zauna can ba sai kin dawo nan ba"

Sultan da ya fuskanci inda Taheer ya dosa ne ya saki wata siririyar dariya, ya dauki wani dan qaramin kara ya saka a wuta, ya kafe kallon shi a cikin wutar.

Sai da Mubaraka ta bacewa ganin su sannan, Sultan ya ce,

"Ka dena bata ran ka aboki na, ita mace irin wannan allura ce cikin ruwa, sai ka ga mai rabo ya dauka, mu yi addu'a mu barwa Allah komi"

Taheer ya dan ji kunya da nauyin fadan da ya yi, sai kawai ya miqe ya bar wajen.

Tun da sultana ta leqa ta ga ana ta shara, ta ji gaban ta ya fadi, domin abinda take shirin aikatawa zai iya jawo mata mummunan hukunci wajen Lawwali, amma ta riga ta yi niyya, ba zata fasa ba.

Sauri ta yi ta koma d'akin, ta taya shi shirya wa, kaya masu kyau ta daukar masa, sannan ta d'aukar wa Mubaraka ma wasu kaya masu kyau daga nata dan ta saka, sun yi kyau sosai, Lawwali gaba d'aya ya sauya, nutsuwa kamala, da hankali sun samu wajen zama a jikin shi.

Su na kammalawa suka yi wa sultana sallama ya kama hannun Mubaraka, suka fita, mota suka shiga su na d'agawa juna hannu, Sultana kuwa yaqe take ta yi, tafin hannu da qafar ta sai zufar tashin hankali suke fitar wa.

Motar su na barin harabar wajen, sultana ta fad'a dakin su, ta tattaro, laptops wayoyi, da duk wani qundin ajiya, ta yi waje,direct d'aya daga drums din da ake kunna wuta a qona shara ta nufa, ta fara zuba su, d'aya bayan d'aya, ta na zuba disc na qarshe a wuta ta ji qarar motar Lawwali, wani irin tsoro da tashin hankali ne ya shigi sultana, sai da cikin ta ya murda, ta dafe marar ta, ta durqusa a wajen.

Ta na nan duqe Lawwali ya nufo ta, cike da tsananin bacin rai, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, hannun shi dunqule ya nufe ta, bakin ta ne ya fara rawa, hawaye na zuba, hannun ta dafe da marar ta, ta ke ja da baya, tana kad'a masa kai, leqawa ya yi, ya ga yanda abubuwan da ta sa ke ci da wuta, ga baqin hayaqi ya turnuqe wajen.

Cikin tsawa da hargowa ya nufe ta ya daga hannun shi zai kife ta da mari, ya ji an riqe hannun, ido suka had'a da Mubaraka, na zubar da hawaye, cikin tsoro, abinda bata taɓa ji ba game da yayan nata, dan ta san ba zai taba cutar da ita ba, amma yanayin shi a yau ya firgita ta.

Hannun shi ya sauke ya fara kaiwa da komawa, ya na shafa kan shi da hannun damar shi, cikin bacin rai ya kalli inda Sultana ke durqushe ta na kuka, Mubaraka na lallashin ta, ta na so ta d'aga ta tsaye.

"K..k...kayi hankuri....bb.ba zan iya bari ka aikata...abinda ka ke da niyya ba...ba domin kar mahaifi na ya shiga hannun hukuma ba,...ko kar a hukunta shi...ya cancanci dukkan hukunci...ba zan iya rayuwa ba kai ba...zan mutu a duk sanda na budi ido na ga babu kai....dan Allah kar ka yi abinda ka ke shirin aikatawa....na qona shaidun ne saboda a kowannen su ka na ciki,..."

"Yi min shiru ! Kar ki kara magana ! Kin ci amana ta Sultana, ba zan yahe miki ba,ke qona ne saboda ba ki son wancan azzalumin mahaifin na ku ya karbi hukunci a hannun hukuma ko? To ki sani, a yanzu in na je na bada shaida, na kawo jami'an tsaro nan, suka ga komi, hakan ya wadatar, mahaifin ki ba shi da wani qarfi a gwamnati a yanzu, har an dora wani a madadin shi, ba zai iya mulkar jama'a ba, da shayayyar qahwa, sultana me ya sa ki ka ci amana ta, bayan na yarda da ke, wadannan bayin Allah da muka zalunta shekara da shekaru ki na zaton sun yahe muna ne? Kin san yanda muka lalata rayuwar su ne? Har yanzu ina jin zahin lalata qaunata da aka yi, kamar mashi a qahon zuci, su fa? Ki na tunanin sun mance ne? Ko kuma ba su jin zahin abun? Sultana me yasa ki ka aikata haka? Me ya sa?"

Naushi ya kaiwa drum din da ke ci da wuta, ya fadi qasa, wutar ta yi taratsatsi, mutanen da suka taru a wajen yanzu duk sun fuskanci me Lawwali yake magana akai, zuciyar su ta karye matuqa da jin kalaman shi, ashe shi ya sa ya maida wasu ga iyayen su, kuma ya ke qoqarin ba wa wasu wanda suka rage a wajen ingantacciyar rayuwa, ashe ya na so ya miqa kan shi da duk mai hannu a kamen su ga hukuma? Lallai zuwan sultana cikin su alkhairi ne,domin ta sa Lawwali ya sauya daga Oga Makashin mutane zuwa Auwal mai tausayi da sanin ya kamata.

Mubaraka ce ta jingina Sultana jikin wata bishiya, sannan ta tsaya a gaban Lawwali, cikin zuciyar ta cike da tsoro, amma ta na qoqarin nemo jarumta irin tashi ta sanya a fuskar ta.

"Yah Auwal ba laifin Aunty Sultana ba ne, ni ta na bata shawara a qona, saboda na gan su, kuma na yi tunani in wani abu ya same ka wa nake da shi a duniya? Ka riga ka tuba ga Allah, ka kuma dau duk matakin da ya dace dan ganin ka gyara abinda ka bata, kana tunanin su hukumar da za ka kai kan ka wajen su, mutanen kirki ne? Ko ka na tunanin in aka binciko lehin da wasun su ke aikatawa za a bar su a raye ne suma? A yanzu yanda hukuma ta lalace mutane na gari ma da ke cikin ta ba su da qarfi,neman durqusar da su ake kullum, Yah Auwal kai wa Allah ka fahimci Aunty Sultana, ba ta da lehi, ba ta so ta fadi gaskiya ne ka ji haushi na, shi ya sa tai shiru"

Hawaye ne kawai ke zuba a idon Sultana,tare da jin qauna da soyayyar mubaraka na ratsa ta, tabbas wannan dalilin na cikin dalilan da ya sa Lawwali ke son ta, ta na da hankali da hangen nesa.

Lawwali bai ce komai ba ya bar su a tsaye a wajen,ya tafi dakin shi ya dauki wayar shi da ya manta, ya shiga cikin daji sosai, dan so yake ya yi nesa da su, ya na so ya kad'ita.

*Ohhhh Oga akwai son kai, dake Mubaraka ce ya yi shiru, amma da zai kai wa yar mutane duka😏*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH


PAGE 55:



Mubaraka da Sultana kuwa d'aki suka koma, bayan Mubaraka ta taimakawa Sultana ta zauna a bakin gado, Sultanan ta kalli Mubaraka ta ce,

"Mubaraka me yasa kin ka yi wa yayan ki qarya, bayan a kullum shi na yabon ki akan rashin yin qarya? Me ki ke tunani in ya gano baki da hannu a abinda ni na aikata ba ke ba? Gashi yanzu kin rusa muku tafiyar da ki ka jima da burin ki na son  ya amince ku yi,"

"Babu komi aunty na,nasan ba zai iya kwana shi na hushi da ni ba, zai sakko ne, ni kuma ba zan iya jure ganin ki cikin halin baqin ciki ba, zai fahimce ki, bashi lokaci ya yi tunani, haka yake, ya na da saurin hushi, amma da ya fahimci gaskiya ya na saurin sauka"

"Allah ya sa ya sauka da wuri, ba zan iya jure fushin shi ba, amma me ya sa kuka dawo?"

"Waya tai yam-mance, shi na mun ka dawo dauka, ya shiga dakin yaga waccan locker a bude, shi ne na ga hankali nai ya tashi,ya na neman ki"

Murmushi Sultana ta yi, ta kalli Mubaraka ta ce,

"Na gode"

Su na nan zaune kamar marayu ya dawo,  a rayuwar Lawwali ya tsani rashin cika alqawari da cin amana.

Ya san ya yi wa Mubaraka alqawarin kai ta gida,ga kuma Sultana ta ci amanar shi, dan haka dole ya dau mataki,

"Ki taho mu tai,...ke kuma na janye zuwan ku gida a gobe, har sai na gano gaskiya game da abinda kin ka yi min"

Murmushi mai quna ta yi, akwai zafi, wanda ka ke so, ka yarda da shi ya zama shi bai yarda da kai ba.

"Babu komi, Allah ya sa ka gane irin son da nake maka, ba zan yi komai dan na cuta maka ba"

Kallon cikin idanun ta ya yi, nan da nan na shi suka fara sanyi, da hanzarin shi ya bar dakin,tare da fadin

"ki taho mu tai"

motar shi ya shige, ya na zaune ya na jiran Mubaraka,  qasan zuciyar shi na ayyano masa fuskar Sultana,mai cike da ban tausayi, da tsantsar soyayyar shi, ba ya so ya yarda da cewar amanar shi ta ke son ci, amma ya kasa dauke hankalin shi daga abinda ta yi din, anya ba da gaske saboda Daddyn su ta qona ba?

Mubaraka ma bata b'ata  lokaci ba ta bishi , ta na shiga ya bar wajen da gudu, ta waya ya bada umarnin a shiga wajen Sultana a duba ta, a ga me ya sa ta ciwon ciki.

Sun isa gidan Dan Talo da misalin sha daya na rana, har a wannan lokacin mazaje masu zaman banza na zaune, a jikin katangar gidan,a jingine da gini, su na shan hantsi, ana ta zuba qarya,domin abun na su ya wuce hankali .

Hango mota mai kyau suka yi ta na tunkarar su, nan da nan kuwa a cikin su aka samu wani maqaryacin ya ce ai ya taba ganin me motar har sun ma gaisa rannan, wasu sun yarda wasu sun qaryata, tunda sun san junan su.

Dan Talo dai sai gwale ido ya ke, ya ga mamallakin motar, domin dukkan alamu sun nuna gidan shi motar ke tunkara, nan da nan kuwa ya miqe ya kade rigar shi da ta
Showing 117001 words to 120000 words out of 150481 words