har da su goyo, su doki, duk haka yake musu wasa indai shi na gida baya gajiya "

"Allah Sarki, Allah shi yi muku albarka"

******************

An sha fama sosai kafin Sultana ta yarda ta auri Yaya Musa, abinda ya sa ta yarda ganin irin yanda yake son Muhammad kamar shi ya haife shi, shi ya ja ra'ayin ta, ta tabbata ba soyayyar nan bace da ake cewa, in zaka so bazawara ka so dan ta, ta tabbata wannan soyayyar gaskiya ce, dan wasu za su nuna suna son dan bazawara, sai bayan aure su yi ta rashin mutunci.

Ba a wani ja dogon lokaci ba aka sha biki, amarya Sultana ta tare a gidan Hajiyan Hansatu, zama suke na mutunta juna, da karrama juna, tare da so da qaunar juna.

Sultana bata taba ganin wani a gidan ya nuna wa Muhammad banbanci ba, daga manyan har yaran, hasali ma wata soyayya yake samu ta daban,saboda yaro ne mai kyau, da kazar kazar kuma ba shi da qiwa.

Yaya Musa ya samu kulawa da soyayyar da yake fatan samu a rayuwar shi,ji yake kamar auren saurayi da budurwa suka yi da Sultana tsabar kulawar da take bashi.

Sultana kuwa a koda yaushe qoqari take ta danne soyayyar Lawwali da ke binne a qasan ran ta dan faranta wa mijin ta mai tsananin son ta.

**********************

Bikin suna ake ta yi, a gidan Hajiya Ikee, Sultana da Hansatu sune akan komai, Dan haka komai ya kayatar ya wadatu, ba wanda ya taba zaton Mubaraka za ta yi qiba, sai ga shi haihuwa daya ta zama masha Allah, wata yar kubul kubul da ita, gwanin sha'awa ,ta samu yarinya mace, an sa mata suna Ayshaa, sunan da Lawwali ke buri ya sanya wa diyar shi, in mace  ce, Sultana tai ta shagwaba ta na fadin an riga ta, dariya suka dinga mata, Mubaraka kuwa ta bata hakuri ta ce,

"Next time ke kuma sai ki haifi Humairah"

Dariya aka sake sanyawa cikin farin ciki, haka sukai ta nishadi, angon qarni na can tare da abokan shi,su na cin abunci.

Tsohon gidan su Sultana da Lawwali kuwa, an maida shi islamiyyar matan aure, an saka mata Suna Muhammad Auwal Qur'anic recitation school, Mubaraka ce ke kula da makarantar da wasu malamai da suka d'auka.

Su Mai Buruji da Lamishi da 'Yabbuga kullum da yamma Jameelu ke kai su ya maida su in an tashi.

Tammat bi hamdu lillah.


Nan na kawo qarshen labarin Oga Lawwali, ina fatan kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min,ya shafe shi cikin rubutu na da zuqatan wanda suka karanta, alkhairin da ke ciki Allah ya bani ladan shi, ya sa al'ummar musulmi su amfani da shi,Allah ya zaunar da ƙasar mu lafiya ya biya wa kowa buqatun sa na alkhairi daga kan 'yan qasar Nigeria zuwa shugabannin mu da su kan su 'yan ta'addan dan a daina kashe kashen da ake yi Ameen.

*Haermeebraerh ce*

(Hamibrah)

*Haermeen Hammah❤️🙈*

*Hameedah Sanusi Ahmad*

*Ummu Fateemah wa Muhammad Muzakkir* ❤️



Showing 150001 words to 150481 words out of 150481 words