kai za su fita, Kamalu dan Mai Buruji ne ya dawo, ya yi fururu da shi, dika dika ba zai wuce sha uku ba, shegen yawo ne da shi,baya son zaman gida sam, dan Uwan shi Jameelu mai shekara sha biyar tun tuni ya koma ya ci abinci, ya kwanta, har wannan lokacin ya na ciki ya na bacci, amma Kamalu zai iya kaiwa sha daya na dare a waje, watarana shi ke rufe gidan.

"Ja'iri,yunwa taddawo da kai gida, da ka samu inda kacci abinci ma na san sai dare aka ganin ka,"

Duqar da kan shi yayi, ya kauce wa dukan da Lamishi ta kai masa, ya na dariya.

Ciki ya shige su kuma suka fita, tun daga nesa suke hango wasu mata guda biyu zaune qasan wata bishiyar darbejiya mai yalwar ganye, da ni'ima, zazzaune suke saman duwatsun da ke wajen.

Daga nesa 'Yabbuga ke wara ido dan ganin sunan atampar da su Lamishi suka sanya,bata samu nasarar ganin qasan ba, saboda an kalmashe an dinke, su na zama kuwa ta kai hannu jikin Mai Buruji da tafi kusa da ita, cikin dabara ta shafi atampar ta na masu sannu da zuwa.

"Sa'idawa, shahwa da kyau wallah, super ta ba komi ba, sabuwar ta mun ka sanya ba kwance ba, ko ita ma ki na saye ne?"

"Yo in da kudin kuturu alkaki ai sai na qasan kwano ko?" cewar 'Yabbuga da ta qule saboda gano ta da suka yi.

"Ahayyyyeee,Allah gani inji gurguwa, watarana kau kuturu zai hadiyi yawu da quda,dan wani alkakin na sarakai ne,ba na siyan gama gari bane...keni rabu dani da d'umin banza, bamu labari mi na na ki ka son hwada mana dazu ki ka ga dodon ki,ki ka gudu"

Wadda ake kira da Ta Yahai (Yahya kenan) ita ce cikin dariya ta ce,

"'Dana ya shigo gari kenan, dan albarka me maganin munahukan shiyya"

Dariya suka sanya, Yabbuga kuwa rai ta bata, dan ta san ci mata fuska suke, sun san yanda take tsoron Lawwali.

"Ke rabu da Ta Yahai, bamu musha" In ji Lamishi da ta qagu ta ji me' Yabbugan zata fada masu.

Zama ta gyara dan jin an sosa mata inda ya dame ta da qaiqayi.

"Hummm na taba ku da alheri, kishiya ta taɓa kishiya da bakin wuta....jiya akai dirama a kwarkwadar mu, tsakar dare nijji ana ihu, ana bada hankuri, nittashi zaune ni da Dan Jumma, ko da mun ka saurara, ashe mutuniyar aka liqa wa mugun kashi,"

"Kaiii wanga mutuni ba dan Sunnah bane, mi tai Mai halan?" Cewar Mai Buruji da ta matsa daf da Yabbuga tsabar son jin gulma .

"Yo ai abun ba sabo bane, sun yini ba bu ko kwayar hatsi,dare ya yi,ya tai amsar haqqi nai ta hana, shi ko yabbuge banza, ya amshi abi nai, ya barta nan ta na kuwwar banza"

"Ohhhh wanga shi aka kira qarfin hali, a dake ka kuma a hana ka kuka, gaskiya mutunin ga azzalumi na" Lamishi da ta qi jinin ta ji ana wulaqanta mace ta fadi hakan, lokuta da dama ji take da ace su na magana da Hansatun Isa da sai ta mata magana, ta koya mata yanda zata kwaci 'yancin ta wajen Isa, ko ya hakura da mugun halin shi su zauna lafiya.

To amma Hansatu ta kame kan ta, mace ce mai kame wa matuqa, da kiyaye dik wani abu da zai hada ta hulda da su Yabbuga, tunda ta san halin su.

Su na nan su na gulmar ta, ta na gida ta na fama da matsanancin ciwon qirji, ba komai ne ya kawo mata shi ba, illa rashin cin abinci, yaran ta ta kalla guda uku, biyu mata ,daya namiji, suna ta kai loma, hannu baka, hannu kwarya, akan qanzon da ta masu fate da shi.

Lallabawa ta yi ta dan debi loma daya ta kai bakin ta, wani irin zafi da murdawa qirjin nata ya yi, sai da ta durqusa,tare da rintse ido, hawaye ne suka sauka mata, da sauri ta share,dan kar yaran su gani,bata samu nasara ba kuwa, qaramin yaron ta mai shekara hudu ya ga sanda ta ke share hawayen,dakatar da cin abincin ya yi, ya ce,

"Umma sannu, qirjin ki na ka ciyo?"

Cikin murmushin yaqe ta ce,

"Eh shi na ka ciyo Ahmad, amma yayi sauqi, kaga Ni ma har na tashi ? Maza ka ci abincin ka yaron kirkin Ummaa,ku ta tahiya makarantar Allah"

"To Umma"

Amina da Bilkisu ma sannu suka mata, sannan suka dauki dan sauran faten da suka rage, suka aje a gaban ta, suka ce sun qoshi.

"Abincin da ba shi da yawa, ku canye shi maza, kahin ku dawo,inshaa Allahu zan sama mana wani abun, ku canye ku tafi makarantar Allah maza"

Qin ci suka yi, tare da barin kwanon a gaban ta suka tafi da gudu wanke hannu, suna gama wankewa, Amina mai shekara goma,ta shirya Ahmad cikin wasu yagaggun uniform din da sun dage masa, ita kuma hijabi kawai ta saka tamiqawa Bilkisu mai shekaru takwas nata hijabin, su na kammala sakawa suka yi wa umman su sallama suka fita, bakin su dauke da addu'a .

Ta gaban su Mai Buruji yaran suka wuce, sai da suka gaishe su sannan suka tafi,amsawa sukai su na bin su da kallo.

"Dazu fa Baban su har da shi a garkar mu, wajen cin abinci"

"Ai wadda kika san dan shi d'ai muka zuwa aiki,kullum shi na garkar mu, da ya qare cin abinci shi tai yawo"

Yabbuga ce ta karkace zata yanko wata gulmar Isa ya taho zai shige gida,cikin izza da isa da taqama ya ke tafiya , wanda be san shi ba zai rantse wani namijin azziqin ne.

Har su na rige rigen gaida shi ,juyawa ya yi, ya amsa tare da tsokanar su Lamishi .

"Ah ah matan Dan Talo kenan, irin wanga gayu haka awaz-zaku biki? Ko dake masu hidima gidan Gwauna ai dole ku wataya "

Murmushi suka yi, su na irin abun nan na mata in an yabe su, Yabbuga kuwa tsaki ta ja, sannan ta ce,

"Haramun dai, ka tsaya yabon matan wani, ka baro ta gida ba yabo"

"Yabbuga kishi takai da ku wallah, kun San bata iya ganin wani ya yi abu, batai ba"

Dariya suka sanya har da shewa, ya shige gida,ya bar Yabbuga da mita.

Kafin ya qarasa shiga ya daure fuska tamau kamar ba shi ne ya gama hira da matan wasu a waje ba.......

A GARIN MU






WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









PAGE 4:


Jin motsin shi ne ya san ya ta miqe wa da kyar, hankalin ta tashe, domin shi din kamar wani dan aiken mutuwa n ne a gare ta, rashin fitar ta tsakar gida zai iya ja mata masifa a wajen mijin nata da take tsananin so da qauna.

Murmushin yaqe ta sanya a labban ta, tare da yi masa sannu da zuwa, bai amsa ba, sai shura buta da ya yi da qafar shi ta hagu, cikin wani irin mummunan yanayi ya juya ya kalle ta, yawu ta hadiya da kyar, cike da tsoro, bakin ta na rawa ta ce,

"Ka yi hankuri, su Amina na sun ka wanke hannu, Na....naaa manta ban zuba ruwa ba"

"Zaki debo min ruwa ko surutun banza za ki tsaya yi min?"

Da sauri ta tafi daukan butar, kafin ta sa hannu ta dauka ya tura mata da qafa, dan baya ta ja saboda kar ta bige ta, sannan ta duqa ta dauki butar, wajen diban ruwan daidai inda yake a tsaye ne, ya diba kawai, amma sai ya wahalar da ita.

Ta na gama zubawa ta duqa ta fara zuba masa, qamshin miya ta ji a hannayen shi a lokacin da ya tara su gaban ta dan ta zuba masa ruwa.

Murmushi mai ciwo ta yi, ta tabbata yau ma ya ci abinci a waje, ba tare da ya damu da ita ko yara sun ci ko basu ci ba.

"Baban Amina, nicce akwai dan kuddi wajen ka na dahwa muna abinci?  Yau kwana uku ba mu ci abincin kirki ba, dazu ma qanzo na nissamo gidan Yabbuga niddahwa mun ka ci, kuma da alama yaran nan basu qoshi ba"

Hannayen shi ya sanya a qugun shi ya na kallon ta, irin kallon nan mai kidimar da wanda ake kallo, ta gigice matuqa, dan bata san me zai je ya zo ba, amma koma mene ne, bata da zabi, dole shi ne zai kula da su, shi ne zai yi mata duk wani abu da take buqata ita da yaran su .

"Kin raina Ni ko? Na ce kin raina Ni ko? Kin fara min tambayar titsiye ko? To ina da kudi,kin gan su, ba zan bayar ba"

Hannu ya sanya a aljihun shi ya zaro dari bakwai, ya nuna mata, sannan ya miqa su daidai fuskar ta,

"Ko zaki kwata ne? Tunda na ga kin yi qarfin halin yi min magana yanzu, ban sani ba ko kin yi qarfin duka na ki amshi abu a hannu na ne"

Kada kai take ta yi, tare da fadin,

"Ah ah, ka yi hankuri, ba haka nika nuhi ba"

"Hansatu , Hansatu, Hansatu ki kiyayen, kar ki bari na juyo kan ki ba zaki ji dadi ba"

Duqar da kan ta tayi, tare da share majinar da ke diga daga hancin ta, saboda kukan zuci da take,

Daki ya shige, ran shi a matuqar bace.

Babban abinda ya ban mamaki, haushi, da tausai shi ne, kwano ne ajiye a wata shimfida, abinci ne a ciki, kalar wanda ta bawa yaran ta da rana, duk yunwar da take ji, bata iya ci ba, sai da ta aje masa.

Dan mugunta irin ta Isa dauka ya yi, ya fara ci, sai da ya cinye tass ya sude kwanon ya yi fatali da shi ya bar gidan.

Qarfe biyar da rabi, ta rasa ya zata yi, dan haka mayafi ta dauka, ta yafa a saman kan ta, sannan ta saka takalmin ta silifa da ya sude, ya ke qoqarin bulewa.

Jan qofar gidan ta yi, ta nufi dandalin gulmar su Lamishi, duk wanda ya kalle ta da kyau zai tabbata ta sha kuka, amma ya zatai, ba zata iya boye yanayin da take ciki ba, tunda mai rufa mata asirin ya tone shi kowa ya san halin da suke ciki,  (ba mai rufa asiri sai Allah).

Ta na zuwa ta Gaishe su, dikkan su amsa wa sukai, cikin zumudin son jin me ya faru, ba wai dan su taimaka mata ba.

Shiru ta yi, can suka ci gaba da hirar su, amma hankalin su na kan ta, gani ta yi lokaci na tafiya, cikin sanyin murya ta ce,

"Uhmmm... Nicce ko akwai wadda ke da wanki cikin ku? Ku kawo na hwara na kuddi, amma za a hada da kuddin wanki da klin da toka(sabulu) "

Kusan a tare suka hada baki suka ce babu, ji ta yi kamar an daki zuciyar ta, da me za su ci abinci dare?

"Ko wani aiki ba ku da shi? Wanda zan yi ku biya Ni?"

Lamishi ce ta ja ta  gefe, ta ce,

"Ina da wankau, amma fa na yau ne kawai zan baki, ba wai kullum zaki zanka(dinga) yi min wanki ba"

Kamar ta durqusa a qasa ta gode mata, haka Hansatu ta hau godiya.

Gidan Dan Talo suka koma , Lamishi ta bata wankin, ta bata kudin omo da sabulu, ta biya ta ladan wanki dari uku, godiya ta dinga yi har da kwallar ta.

Ɗaukan wankin ta yi a ka ta yi shago, ta auni wake, dan ya fi arha, kuma in ta dafa za su jima suna shan ruwa in an ci, ta sai man ja ta sai  maggi, ta sai omo da sabulu, sanan ta yi gida.

A hanyar ta ta komawa gida, ta ga dandalin su Lamishi suna nan suna hira, kafin ta qarasa ta ji Lamishi na basu labari  taimakon da ta mata, ran ta ya baci, amma ba yanda ta iya, wanda ya ajiye ta shi ya ja mata komai, ta na yin kusa da su sukai shiru, kamar ba su ke magana ba.

Gidan ta ta shige, ta ɗora tukunya ta wanke wake ta jiqa tokar murhu kadan ta zuba dan ya dahu da wuri, itacen ba yawa, fatan ta Allah ya sa ya dahu da wuri, ba dan yaran sun kusan dawowa ba da jiqa waken zata fara, ta rage asarar ice.

Bokiti ta dauka ta je ta roqi Yabbuga akan za ta debi ruwa a rijiyar gidan ta, cikin daure fuska ta ce ta je ta diba, godiya ta yi, ta shiga ta dinga jidar ruwa, qirjin ta na matsanancin ciwo, amma ba yanda za ta yi, dole hakuri za ta yi, ta nemawa yaran ta abin da za su ci.

Ta na fitowa daga gidan Yabbuga ta ji ta na fadin.

"Kuuu ban baku labari ba, kun kuwa san an yi baquwa a shiyyar ga tamu? Humm in kun gane(in kun ganta) ta baqa awab-baqar talle (kamar baqar tukunyar miya) , mijin ta ko kyakkyawa, nicce wanga mi yaggani da ya kwaso mace hakan ga awak-kuddi (kamar kudin shi basu cika ba) nai basu cika ba"

Dariya suka sanya da shewa , suka tafa,

"Yabbuga idon duniya, ta wanne bangare gidan yake gobe in su Lamishi sun taso aiki mu tai ganin gida ?"

"Can bayan gidan su Lamishin ne ai, sai kun ga gidan , wayyooo aljannar duniya kenan, gidan da nika mahwalkin samu Allah yabbatar, babu komi, su ci anan, mu ci a can"

"Ke haba na gane gidan, gidan nan me dan banzan kyau, ashe an tare"

"Shi hwa ni ka batu"

Lamishi na qoqarin magana Yabbuga ta jiyo qarar machine din Dan Jumma, da wata iriyar alkafura ta hantsila ta fada gidan ta, dariya suka fara yi, suna fadin ,

"Shegiyar za ta yi tsiya kenan,duk ka ga Yabbuga ta shiga gida bata son Dan Jumma ya gan ta nan, to akwai tsiya"

"Ina yini Dan Jumma ?"

Cikin daure fuska ya amsa ya shige, bai jira jin me za su fada ba, cikin qunar rai, dan ya san dole Yabbuga ma na wajen, sai dai guduwa ta yi da ta ji shi.

Sallama ya rangada, tare da jingine machine din shi, ya cire yar ledar da ke jikin hannun machine din, ya taka zuwa bakin qofar dakin nasu, kwance take abun ta, ta na jin shi ya na sallama ta qi amsawa.

Murmushi ya Yi, dan kuwa ya san halin kayan shi, ajiye ledar ya yi, ya zauna tare da bude kwanon abincin da ke gaban shi, shinkafar ce dai da miya, kullum abincin kenan, in an sauya kuwa to tuwo ne, in ya kawo taliya ko wani kalar abincin sai ta dafe lokaci daya ta raba wa qawaye ta nuna masu itama ana cin dadi gidan ta, ba wai dan ta samu lada ba.

Budewa ya yi ya fara ci bayan ya yi Bismillah,

"Au ka na gani ina hushi ba za ka kula Ni ba ko? Tauu ya yi, ci abincin ka ka qoshi da kyau, ya yi" ta juya baya ta na zumbura baki, ita a dole fushi take.

Dan Jumma bai kula ta ba, sai da ya ci abincin shi sanan ya tattara hankalin shi zuwa gare ta......

A GARIN MU








WRITTEN BY HAERMEEBRAERH










PAGE 5:





"Ina sauraron ki sarauniyar mata, mi am-matsalar ki yau Kuma?"

"Auuu ni ce matsalar ma ko? Tau ya yi"

"Kin dai san ba haka nika nuhi ba ko? Ina so na San damuwar ki, da har zan sallama ki qi amsa min ki na musulma"

"Suhwa nika so"(super na ke so.. Atampa)

"Me ne ne haka nan? (Me ne ne hakan)"

"Atanhwa suhwa nika so," (atampa super nake so)

"Ai ko aiki ya gane ki wallah, ni da nike qaramin ma'aikacin da rabo na da albashi yau wata biyu, haka d'ai sai ni kama sai maki wata super Dan dai ban da hankali ko?  To mi za mu ci in kin Sanya super?"

Kuka Yabbuga ta saka, har da Kiran ta shiga uku, tsiyar auren talaka kenan, bata rai Dan Jumma ya yi sosai ya kalle ta,

"Ni ki ke kira da talaka yau Kuma Yabbuga? Lallai mace akwai ta da mance alkhairi, ke manta sanda nike da walwala, ke mance sanda nike da azziqin da kk Shan gatan da ba bu ya ke a cikin tsarar ki? Ke fa ba qaramar yarinya bace, karki manta bara waccan anka kai Kareema d'aki, yanzu haka ciki gare ta, kin kusa kai wa ga jika, shi na ki ke Wagga baqar tabi'a"

"Ni ke baqar  d'abi'a ko kai? Yanzu ace yar super ga ba ka iya sai min? Shin ta Ina ka bi ka shigo gidan ga? Ba ka ga su Lamishi a waje bane?ko ba ka ga irin tuwahin da ke jikin su ba ne? Nan Nan Isa da yaggane su sai da ya tsaya ya yabe su, ni matar ka Kuma maqotan shi kallo ban ishe shi ba"

Wani irin zabura Dan Jumma ya yi, tare da kallon Yabbuga a yanayi na tashin hankali.

"Mi na na ki ka ce, Isa ya gane  ku bai yaba tuwahin ki ba ,shi ka banna maki rayuwa hakan ga?(Isa ya gan ku be yaba kayan ki ba shi ke bata maki rai?) Ashe dama Isa ki ka aure ba Dan Jumma ba? To ki tai Isa shi sai maki super Yabbuga na Yi masallaci"

"Walle ba ka Isa ka juyan magana ka tafi ba, ka San ba haka nika nuhi ba, super ko sai ka siye ta gidan ga, kahin ka ga hwari na,"

"Irin wanga halin da ki ke shi Kareema ta koya, daga yin aure mijin ta ya kawo qara ya hi sau bakwai, kwanaki ba koro ta ya yi ba da ya gaji da bani bani da sai min? Da girman ki amma ki na wanga mummunan hali, ba lehin ki na ba, lehi na na, da a baya niyyi zamanin sai maki duk wani abu da aka yayi, maimakon yanzu da Banda shi ki hakura ki San na kyautata maki a baya, shi na kk hango na sama da ke, se ki fada min, da su Lamishin Basu aiki gidan Gwauna Ina na zasu samu kwancen tsohuwar super ma balle sabuwa? Sannan  da ki ke gasa da Lamishi, ai Lamishi ta ciri tuta tunda ta iya zama da kishiya, me ya sa baki gasa da ita ta nan ba? Gashi can su na zaune lahiya kamar Yaya da qauna"

"Babbar batasin Nan, ni ka ke kalla ka yi min batun kishiya Dan Jumma? Ashe ka daina so na? Ka San
Showing 3001 words to 6000 words out of 150481 words